Kotun daukaka da ke zamanta a Jihar Legas a ranar Juma’a ta yanke wa Sanatan da ke wakiltar mazabar Delta ta Arewa a Majalisar Dattawa, Peter Nwaoboshi, daurin shekara bakwai a gidan yari.
Sannan kotun ta same shi da kamfanoninsa guda biyu, Golden Touch Construction Project Ltd da Suiming Electrical Ltd, da laifin aikinta mu’amala ta kudade ba bisa ka’ida ba.
- Kotu Ta Hana Ganduje Ciyo Bashin Biliyan 10 Don Sanya CCTV a Kano
- Kiki-kakar Mallakar Makami A Zamfara…
Hukuncin na kotun daukaka karar na zuwa ne bayan samun nasarar daukaka kara da hukumar EFCC ta yi don kalubalantar hukuncin da Justice Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya da ke Legas, ya yanke a ranar 18 ga watan Yunin 2021, inda ya sallami wanda ake kara tare da wanke shi bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka kunshi zamba da halasta kudin haram.
EFCC ta gudanar da wadanda take kara su uku ne bisa mallakar kadara mai suna Guinea House, da ke layin Marine, a Apapa, Lagos, kan kudi miliyan N805. Daga cikin kudaden da aka biya dillalin muhallin, kimamin naira miliyan N322 da Suiming Electrical Ltd suka tura a madadin Nwaoboshi da Golden Touch Construction Project Ltd, ana zargin kudi ne da aka samu ta hanyar zamba da damfara.
Shi dai Alkali Aneke a shekarar da ta gabata, ya sallami karar ne bisa dogara da cewa masu shigar da kara sun kaza kawo kwararan hujjoji kan wadanda suke tuhuma don haka ya sallami karar a wancan lokacin.
Sai dai a hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke a ranar Juma’a, ta ce masu shigar da kara sun tabbatar da kwararan hujjojin da suka dace kan wadanda suke tuhuma, kan haka ne kotun ta samu wadanda ake zargin da laifi tare da yanke hukunci a kansu.