Kotun daukaka kara da ke Abuja, ta yi watsi da daukaka karar da Sanata Aishatu Dahiru Ahmad Binani, ta shigar tana mai kalubalantar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da hukumar zabe (INEC) da jam’iyyar PDP.
A matakin bai-daya da alkalan kotun uku bisa shugabancin Mai shari’a T. O. Awotoye PJ, suka yanke sun yi watsi da bukatar Binani tare da tabbatar da nasarar zaben Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin gwamnan Jihar Adamawa.
Kotun daukaka karar ta ce kotun sauraren kararrakin zaben jihar, ta yi hukunci bisa gaskiya kan koken da ‘yar takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar APC ta shigar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp