Mai shari’a Inyang Ekwo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya ki amincewa da bukatar gwamnatin tarayya na mika mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na kasa Abba Kyari da aka dakatar zuwa kasar Amurka.
Kotun ta ce neman mika shi, cin zarafi ne ga kotun, bisa hujjar cewa Kyari ya riga ya gurfana a gaban wata kotun Nijeriya.
Hukumomin Amurka sun nemi gwamnatin Nijeriya da ta mika Kyari dangane da alakarsa da wani dan damfara na kasa da kasa, Ramon Abass, aka Hushpuppi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp