Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci Monguno a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya jagoranci rajistar yara 4,229 zuwa makaranta, ciki har da marayu, wadanda aka kashe iyayensu a rikicin Boko Haram a sassan Arewacin Borno.
Aikin rajistar da akai a ranar farko (Lahadi) an yima yara 4,229, ana sa ran za a yi wa yara 7,000 a karshen wannan Litinin rajista, a kashin farko.
Yaran masu shekaru tsakanin shida zuwa 13 an musu rajista ne a makarantun firamare da matsakaiciyar sakandire, an yi amfani ne da matsayinsu na karatunsu kafin fara hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram da ya raba yaran da makarantun su a kananan hukumomin Monguno, Kukawa, Guzamala da Marte da ke arewacin Borno.
Bayan hare-hare da dama da aka kai kan al’ummomin kananan hukumomin tun a shekarar 2014, dubban al’ummomi sun tsere zuwa garin Monguno don zama a sansanonin ‘yan gudun hijira na tsawon shekaru, inda yara da dama suka rasa makaranta sakamakon hakan.