Kotun sauraren karar zaben ‘Yan Majalisun Tarayya da na Jiha ta fara zama a Sakkwato a yau Litinin.
A zaman kaddamarwar, shugabar kotun ta (1) Mai Shari’a Josephine Oyefeso ta bayyana cewar kotun ta na da shari’u 15, wato takwas na Majalisun Tarayya da bakwai na Majalisar Jiha.
“A bisa ga sashe na 285 (6) na Kundin Tsarin Mulkin Kasa na 1999, kotun ta na da kwanaki 180 daga ranar da aka shigar da kara domin zartas da hukunci.”
Shugabar wadda ta tabbatar da cewar za su yi gaskiya da adalcin shari’un kuma a cikin hanzari ta kuma yi kira ga lauyoyi da a kauracewa dubaru domin bata lokaci. Haka ma ta bukaci hadin kan lauyoyi da masu kara da wadanda ake kara domin kammala sauraren shari’un a cikin lokacin da aka shata.
Kotun ta na da Josephine Oyefeso, Mai Shari’a daga Babbar Kotun Lagas a matsayin Shugaba, sai Khadi Abdullahi Sa’idu Usman daga kotun daukaka kara ta shari’ar Musulunci ta Birnin Tarayya da Mai Shari’a Eze Eke daga Babbar Kotun Jihar Imo a matsayin mambobi na 1 da na 2.