Daga ranar 18 zuwa 19 ga wata, za a gudanar da taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya a birnin Xi’an, hedkwatar lardin Shaanxi na kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne zai shugabanci taron, wanda zai samu halartar shugabannin kasashen Kazakhstan da Kyrgyzstan da Turkmenistan da Uzbekistan. Taron dai zai kasance irinsa na farko tsakanin shugabannin kasashen shida cikin shekaru 31 da suka wuce, tun bayan kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, don haka yake jawo hankalin kasa da kasa.
Yersultan Zhanseitov, manarzaci a cibiyar nazarin tattalin arziki da siyasa ta duniya a kasar Kazakhstan, ya ce taron zai bude sabon babin dangantakar kasashen nan biyar na tsakiyar Asiya da kasar Sin, wanda kuma zai samar da sabon karfi ga hadin gwiwarsu, ana kuma fatan ganin samun nasarar taron.
Shi kuma Shoazim Shazamanov, shehun malami a jami’ar nazarin harkokin kasashen gabashin duniya ta kasar Uzbekistan da ke birnin Tashkent, yana ganin cewa, taron na da muhimmiyar ma’ana, ganin yadda kasar Sin ta zama abin koyi ga kasashen tsakiyar Asiya a fannin raya manyan ababen more rayuwa da ilmantarwa da al’adu da sauransu. (Lubabatu)