• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kowa Ya Gyara Ya Sani

by CGTN Hausa
2 years ago
Sani

Kasar Sin ta bayyana kudurinta na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da dukkan bangarori, da kuma ba da himma da daukar matakai masu ma’ana a kwamitin sulhu na MDD, domin kawo karshen tashin hankali a zirin Gaza, da aiwatar da hanyoyin warware shirin kafa kasashe biyu, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya. 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta bayyana hake, a lokacin da take karin haske kan kuduri mai lamba 2720 da kwamitin sulhu na MDD ya amince da shi game da rikicin Palasdawa da Isra’ila, inda ta yi kira da a dauki matakin gaggawa na fadada ayyukan jin kai a zirin Gaza da samar da yanayi mai dorewa da kawo karshen tashin hankali.

  • Sin: An Fitar Da Shirin Gaggauta Gina Ingantaccen Tsarin Ayyukan Lissafin Na’urori Masu Kwakwalwa Mai Karfi Na Kasa
  • Kwamitin Kolin JKS Ya Gudanar Da Taron Tunawa Da Cika Shekaru 130 Da Haihuwar Mao Zedong

Idan ba a manta ba, kasar Sin ta kada kuri’ar amincewa da kuduri mai lamba 2720, wanda shi ne kuduri na biyu da kwamitin sulhun ya amince da shi tun barkewar rikicin Falasdinu da Isra’ila. Ta kuma bayyana cewa, kudurin bai zo daidai da yadda kasashen duniya suke tsammani ba kuma yana da wasu gibi da ya kamata a cike su.

A yayin da ya zuwa yanzu rikicin Falasdinu da Isra’ila ya yi sanadiyar mutuwa da raunata dubban fararen hula, kana kuma yanayin jin kai a Gaza ke ci gaba da tabarbarewa, Sin ta bukaci da a aiwatar da kudurin yadda ya kamata, da fadada taimakon jin kai, da samar da hanyar sanya ido nan da nan. A cewar masu fashin baki, matakin na kasar Sin bai zo da mamaki ba, duba da irin matakai da shawarwarin da take bayarwa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, wajen ganin an kawo karshen duk wani tashin hankali dake faruwa a sassan duniya. Har kullum kasar Sin na matukar adawa, tare da yin tir da dukkanin wasu hare-haren da ake kaiwa fararen hula.

Sanin kowa ne cewa, tsagaita bude wuta shi ne abu mai muhimmanci da ake bukata. Kuma kasar Sin ta jaddada kudurinta na yin hadin gwiwa da dukkan bangarori masu kaunar zaman lafiya wajen inganta hadin gwiwa, da daukar managartan matakai don kawo karshen tashe-tashen hankula a zirin Gaza, da aiwatar da shawarwarin kafa kasashen biyu, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya. Wannan ya kara tabbatar da aniya da burin kasar Sin mai kaunar zaman lafiya, na gina duniya mai kwanciyar hankali da kowa zai ji dadin zama a cikinta. Sabanin yadda wasu kasashe ke kara rura wutar tashin hankali, ta hanyar nuna goyon baya ga wani bangare, domin cimma muradunsu na kashin kai, ba kuma tare da la’akari da yadda sakamakon hakan zai haifar ga fararen hula da ma kokarin da ake ba dare ba rana na neman wanzar da zaman lafiya a duniya ba. Amma kowa ya yi na gari don kansu. (Ibrahim Yaya)

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Next Post
Hadin Kan Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Zuba Jari Game Da Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ya Samu Ci Gaba Akai-Akai A Bana

Hadin Kan Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Zuba Jari Game Da Shawarar "Ziri Daya Da Hanya Daya" Ya Samu Ci Gaba Akai-Akai A Bana

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Sani

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.