• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kowa Ya Yi Da Kyau Zai Ga Da Kyau

byCMG Hausa
3 years ago
Tattalin Arziki

Yayin da tattalin arzikin wasu kasashen duniya ke kara fuskantar matsin lamba da tangal-tangal sakamakon manufofin marasa dacewa da tasirin annobar covid-19 da makamantansu, a hannu guda kuma wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar ya nuna cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin yanayi na daidaito da bunkasuwa yadda ya kamata, kana baki dayan karfin kasar ma ya ingantu matuka, haka kuma tasirinsa a duniya yana karuwa a kai a kai.

Wannan ya kara tabbatar da ingancin matakan da mahukuntan kasar ke dauka game da raya tattalin arziki da ma sauran fannoni na ci gaban kasa.

  • Neman Illata Kasar Sin Ya Haifar Da Matsalar Tattalin Arziki Ga Amurka

Alkaluma na nuna cewa, daga shekarar 2013 zuwa 2021, GDPn kasar Sin ya karu da kashi 6.6 bisa dari a duk shekara, wanda ya zarce matsakaicin karuwar kashi 2.6 cikin 100 a duniya, da kashi 3.7 cikin 100 na kasashe masu tasowa a makamancin wannan lokaci, sabanin yadda wasu kasashen yamma ke fama da matsaloli na hauhawar farashin kaya da rashin aikin yi.

Kasar Sin dai ta nace kan inganta ci gaba mai inganci, da bude kofa ga ketare, da sassauta hanyoyin shiga kasuwanninta a bangaren samar da hidima, da bude harkokin cinikayya tsakanin kasashe, da fadada aikin dandalin bude kofa ga waje, baya ga kokarin da take yi na kafa ingantaccen tsarin fadada sashin samar da hidima.

A baya-bayan nan ma firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki, da farashin kayayyaki, da samar da guraben ayyukan yi. Matakan da masana ke cewa, kyakkyawar dabara ce da za ta haifar da da mai ido.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Duk da cewa daidaituwar tattalin arziki ya danganta da yanayin hada-hadar kasuwanni, akwai bukatar a kara azama, wajen rage wahalhalun da sashen hada hadar kasuwannin ke fuskanta, yayin da ake kara fadada harkokin zuba jari, har a kai ga samar da damammakin bunkasa kasuwanni, da karfafa kwarin gwiwarsu.

Idan har ana fatan cimma burin raya tattalin arziki da zai faranta ran al’umma da ma farfado da tattalin arzikin duniya baki daya, ya dace a kara azama wajen kammala manyan ayyuka, da fadada hada-hadar kudade bisa tsare-tsare da aka tanada gwargwadon bukatun cikin gida.

Kana martaba dokokin hadin gwiwar kasa da kasa da muradun juna da sahihin hadin gwiwa, na daga cikin abubuwa da za su taimaka wajen samun farfadowar tattalin arzikin duniya, wanda daga karshe zai taba rayuwar bil-Adama baki daya daga dukkan fannoni. Don haka, duk wanda ya yi da kyau shi ma zai ga da kyau. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
An Yanke Wa Mutane Biyu Hukuncin Daurin Shekara 50 A Saudiyya

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version