An kama wani mai bai wa ‘yan bindiga rahotannin sirri mai shekaru 50, Ado Haruna, bisa laifin haɗa baki da ‘yan bindiga domin yin garkuwa da ɗan yayarsa, Alhaji Bashiru Anas tare da iyalansa a Zariya, Jihar Kaduna.
Duk da biyan makudan kudin fansa har Naira miliyan 13, da sabbin babura hudu, da katin kiran waya na Airtel – Naira 300,000, Haruna Naira 200,000 kacal ya samu a matsayin kasonsa.
- NDLEA Ta Kama Tsoho Mai Shekaru 75 Da Dillancin Ƙwayoyi A Kano
- Dakarun Sojin Sama Na PLA Sun Yi Shawagin Sintiri A Tsibirin Huangyan
Jami’an rundunar lalubo bayanan sirri, suka cafke Haruna, wanda yana cikin wadanda ake zargi da aikata muggan laifuka da jami’in hulda da jama’a na rundunar (FPRO), ACP Olumuyiwa Adejobi, ya baje kolinsu a Abuja.
Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, an rahoto cewa, ya jagoranci ‘yan bindiga uku – Shago Yaro, Tanimu Ayuba, da kuma Lamido Dantajiri zuwa gidan dansa, Alhaji Anas da misalin karfe 1 na dare, inda suka tarar ba ya gida, amma suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa.
An tsare Iyalin har tsawon kwanaki 60 a tsakanin dajin Buruku da Sabo Birni.
Da yake tabbatar da rawar da ya taka a wannan aika-aika, Haruna ya ce, “Ni manomi ne kuma dan banga. Gaskiya ni ne na kai ‘yan bindiga gidan Alhaji Anas. Anas dana ne – dan yayata. Na san daya daga cikin ‘yan fashin da ya ce in nuna musu gidan Alhaji Anas.”