Tsohuwar Jarumar fim a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Mansurah Isa, ta bukaci iyaye da su bayar da ‘ya’yansu a yi samu rigakafin cutar HPV.
Mansurah Isah ta ce ana rigakafin (HPV) domin ceto yaran daga kamuwa da cutar sankarau da sauran nau’in cutar daji.
- Fim Din ‘Princess Of Galma’ Zai Zo Da Wani Bakon Tsari A Kannywood -Jammaje
- Abba Gida-Gida Ya Nada Sunusi Oscar A Matsayin Mataimakinsa Akan Masana’antar Kannywood.
Tsohuwar Jarumar ta yi wannan kiran ne a wata hira da kafafen yada labarai a ranar Lahadi, a Abuja.
Mansura ta ce kwanan nan ta dauki ‘yarta daya tilo aka yi mata rigakafin cutar ta HPV, sannan kuma ta kara da cewa, wannan shi ne karon farko da ake bayar da irin wannan rigakafin kyauta.
A cewarta, a shekarun baya, allurar rigakafin ana sayenta kan kudi Naira 40,000 zuwa N60,000.
Don haka tana son yin amfani da wannan dama a matsayita na ’yar fim kuma ’yar kasuwa mai bayar da agaji da kuma taimakon jama’a ta jawo hankalin jama’a da su sani cewa rigakafin cutar HPV kyauta ce.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp