Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su jajirce wajen ganin sun cusa halaye masu kyau a zukatan ‘ya’yan su.
A wata sanarwa da Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai na ministan, Malam Rabiu Ibrahim, ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana cewa ministan ya yi wannan kiran ne a Kaduna ranar Asabar, a wajen taron laccar watan Ramadan da NTA, FRCN, VON da NBC suka shirya, mai taken “Sauye-sauyen Iyali: Haƙƙoki Da Wajibai a Mahangar Musulunci.”
- Ku Yi Amanna Da Tinubu, Matsalolin Zu Su Zo Karshe, inji Ministan Yaɗa Labarai
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 3 Da Ake Zargi Da Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane A Bauchi
A jawabin nasa, Idris ya ce iyali suna da wani aiki mai tsarki na sanya ƙa’idojin aminci, tausayawa, da gaskiya, tare da sauran ɗabi’u nagari a zukatan ‘ya’yan su domin su tsara halayen su da shiryar da ayyukan su a tsawon rayuwa.
Ya ce: “Dabi’un na ƙwarai su ne ke tafiyar da yaran mu ta cikin sarƙaƙiyar rayuwar duniya, suna taimaka musu su bambance abu mai kyau da mara kyau da kuma bibiyar matsalolin ɗabi’a cikin haske da imani.
“Ta hanyar koyar da waɗannan dabi’u a gidajen mu, muna ba yaran mu abubuwan da suke buƙata don zama masu riƙon amana da sanin ya-kamata a cikin al’umma.”
Ministan ya ƙara da cewa iyali sun kasance ginshiƙin al’umma, wanda ke tattare da addini, ɗabi’u, da al’adu da kuma ginshikin al’umma, wanda ke raya zuri’a mai zuwa tare da inganta zumuncin da zai wuce lokaci da yanayi.
Ya ce ma’aikatar sa na gab da ƙaddamar da Kundin Tsarin Martabar Nijeriya, wanda ya ƙunshi yarjejeniyar zamantakewa tsakanin wannan ƙasar da ‘yan ƙasar, kuma za ta zama wani tsari da manufa ta tsarin ƙimar ƙasa.
Ya ce, “Sabon tsarin, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar a bana, ya ƙunshi Alƙawurran Nijeriya da kuma Ƙa’idojin ‘Yan Ƙasa, waɗanda ke da ginshiƙai bakwai kowanne.
“Gwamnati na da niyyar shigar da waɗannan ɗabi’u cikin tsare-tsare na hukuma, da wanda ba na hukuma ba, da kuma na koyar da sana’o’i don tabbatar da cewa an cusa su a zukatan ‘yan ƙasa.”
Idris ya ce gwamnatin Tinubu ta ba da fifiko wajen aiwatar da tsare-tsare da shirye-shirye masu tallafawa da ƙarfafa iyali da kuma tabbatar da cewa kowane mutum ya samu damar yin rayuwa mai daɗi da kwanciyar hankali, tare da isassun damarmaki don cimma buƙatun sa da burin sa.
“Saboda haka ne gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen samar da yanayi mai kyau ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya ta hanyar aiwatar da sauye-sauyen kasafin kuɗi da na kuɗi da nufin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, rage talauci, da samar da cigaba mai ɗorewa.
“Sauye-sauyen da Mai Girma Shugaban Ƙasa ke aiwatarwa, ba wai martanin da ba a shirya masa ba ne ga matsalolin tattalin arzikin mu; tsare-tsare ne da aka yi tunani a kan su sosai don gudanar da su tare da cikakken Shirin Shiga Tsakani na Jama’a don rage raɗaɗin sauye-sauyen,” inji shi.
Ministan ya ce tare da sake fasalin Shirin Zuba Jari na Ƙasa, an ɓullo da wasu ƙarin tsare-tsare don tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen raba kuɗaɗe ga talakawa da marasa galihu a cikin al’umma, yana mai jaddada cewa daga yanzu za a tantance waɗanda za su amfana da Lambar Shaidarsu ta ɗan Ƙasa (NIN) da BVN ko asusun waya da aka tantance.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu ana gudanar da sauyin yanayi a fannin noma, inda ya ce tawagar sa ta yi mamakin irin nasarorin da ake samu a noman rani a lokacin da suka gudanar da rangadi a wasu al’ummomin manoma a jihohin Kano da Jigawa.
“A ranar Alhamis, na jagoranci Tawagar Sadarwa ta Ƙasa, wadda ta ƙunshi manyan mashawartan Shugaban Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, da kuma manyan daraktoci na Hukumar Wayar Da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), NTA, VON, da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a rangadin aiki a jihohin Kano da Jigawa domin ganin yadda sauyin yanayi a fannin noma ke faruwa a sannu-sannu.
“Ziyarar da tawagar mu ta kai wa Shirin Noman Rani na Haɗeja mai samun goyon bayan Gwamnatin Tarayya da Bankin Duniya ya nuna yadda ake gagarumin noman shinkafa, zoɓo, da alkama, da dai sauran amfanin gona da manoman Jihar Jigawa suke nomawa, waɗanda duk shekara suke noma a bakin tekun kogin Haɗeja da Jama’are. Don Allah, dukkan mu mu rungumi noma da kiwo da fa’idar da suke da ita,” inji shi.