Shahararren dan wasan Hausa na Kannywood Musa Mai Sana’a ya bukaci masu zagin ‘yan Fim da su daina domin suma kamar kowa suna fa ‘Ya’ya da kuma Iyaye.
Mai Sana’a wanda ya yi wannan kiran a wani dan takaitaccen faifan bidiyo ya bayyana cewar yana matukar mamakin yadda ake yi wa masu sana’ar Fin kudin goro wato ma’ana ake aibatasu baki dayansu ba tare da tunanin cewar dole ba za a rasa na kwarai a cikinsu ba.
- Abba Gida-Gida Ya Nada Sunusi Oscar A Matsayin Mataimakinsa Akan Masana’antar Kannywood.
- Abubuwan Da Mace Mai Ciki Ya Kamata Ta Sani
A kowne lokaci idan naji ko na gani a yanar gizo yadda mutane ke aibata mu sai inji a raina cewar gaskiya ba ayi mana adalci ba domin kuwa ba za a taba zamantowa mutanen banza gaba daya ba dole idan aka samu wadanda ba na kwarai ba haka dole idan aka bincika za a samu na kwarai a cikinmu.
Ya ci gaba da cewar ya kamata a yi adalci a wajen magana domin idan aka ce maka ‘yan fim duka ‘yan iska ne gaskiya an yi maka karya domin babu wanda yake da tabbaci a kan wannan.
Ni ba zan iya fitowa a soshiyal media in zagi ko in yi batanci ga wani ba kuma ba zan iya hana masu yi su yi ba amma dai ina jan hankali a kan masu yi mana kudin goro wadanda suke daukarmu duka a matsayin ‘yan iska da su ji tsoron Allah su daina, in ji Mai Sana’a.