Zababben Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bayar da Shawarar Jama’a da kungiyoyi da suke ci gaba da gine-gine a filaye mallakar gwamnati kamar haka:
Na farko ana shawartar Jama’a da su daina aikin gine-gine a filayen gwamnati ciki da kewaye da suka hada da dukkanin Makarantu na Jiha da dukkan wuraren Addini mallakin jihar da asibitoci da makabartu da kuma kwaryar birnin Kano.
- Zaben Gwamna: APC Za Ta Kai Kara Kotu Kan Zaben Gwamnan Kano
- Ba Da Yawunmu Gawuna Ya Taya Abba Gida-gida Murna Ba – APC Kano
Zababben gwamnan ya yi mika wannan shawarar ta hannun kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, a ranar Alhamis.
Idan za a iya tunawa tun gabanin zaben gwamnan Kano yayin yakin Neman zaben gwamnan an jiyo Jagoran Jam’iyyar Sanata Rabi’u Kwankwaso na ikirarin rushe irin wadannan wuraren da gwamnatin Jihar mai ci ta gwamna Ganduje ta cefanar da su.