Shahararren ɗan siyasar nan da ake jin muryarsa kan harkokin siyasa a kafafen yada labarai, kuma jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Abdulmajid Ɗanbilki Kwamanda, ya ce; ya yi dana-sanin tallan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekara ta 2023.
A cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust ta wayar tarho, Kwamanda ya ce duba abin da ya ke faruwa a kasarnan kuma kowa ya ke gani, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu l, ya gaza wajen cika alkawuran da ya yi wa ‘yan Nijeriya da suka fito suka zabe shi.
- Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano
- ‘Yan Nijeriya A Hannun Tinubu Cikin Shekara Guda
Ya ce; a rayuwarsa bai taɓa yin wani abu da ya sa shi yin dana-sani ba irin tallan shugaba Tinubu ba.
Kwamanda Ya ƙara da cewa, yana takaicin abin da yake faruwa a Nijeriya na gazawar gwamnati, amma dole ne sai ya fadi gaskiya duk da shi ɗan jam’iyyar APC ne.
A cewarsa, ƴan Nijeriya suna cikin yunwa, kuma sun fusata da halin da ake ciki, ga rashin tsaro sannan ba kowa ne ya ke iya cin abinci sau biyu ba a rana.
A karshe ya ce yana neman afuwa ga al’umma saboda tallata gwamnatin Tinubu da ya yi akan za ta yi abin kirki amma sai aka samu akasin haka.