Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya shawarci gwamnonin jam’iyyar APC da su mayar da hankali wajen yi wa jama’a aiki, ba wai su fifita kansu ba.
Ya ce shugabanci ya kamata ya zama hanyar bauta wa jama’a da inganta ƙasa.
- Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
- Yadda Kasashen Afirka Za Su Iya Rage Illar Harajin Amurka
Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Gwamnonin jam’iyyar APC (PGF), kamar yadda hadiminsa, Garba Shehu, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce shugabanci na tattare da ƙalubale da dama, amma daidaita su yana iya kawo ci gaba mai ɗorewa a ƙasa.
Ya kuma tuna musu cewa ya bar ofis ba tare da ƙara wani abu a dukiyarsa ba, a matsayin misali cewa shugabanni bai kamata su mallaki dukiya ba yayin da suke kan mulki.
Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna.
Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne.
Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya da girmamawa da gudunmawar Buhari wajen gina demokradiyya da ƙarfafa jam’iyyar APC.
Uzodinma ya yaba wa Buhari saboda salon shugabancinsa, da yadda ya miƙa mulki cikin natsuwa ga wani shugaban APC, tare da aiwatar da shirye-shirye a fannonin tsaro, noma, ilimi da ababen more rayuwa.
Ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, APC na samun kwarjini, kuma ya gode wa Buhari saboda goyon bayan da ya nuna masa a bainar jama’a.
Ya kammala da roƙon Buhari da ya ci gaba da bai wa jam’iyyar shawara da jagoranci domin ganin APC ta ci gaba da mulki da kawo wa Nijeriya ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp