Ministan harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ya yaba wa ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na magance matsalolin tattalin arziƙin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
A yayin wani taron manema labarai da Renewed Hope Ambassadors suka gudanar a Abuja, Olawande ya amince da ƙalubalen tattalin arziƙin ƙasar amma ya nuna ƙwarin gwuiwa kan ƙudirin Shugaban na magance su.
- Sin Ta Taya Murnar Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Nijeriya
- Shugaba Bola Tinubu Ya Naɗa Sanata Bashir Lado Mai Ba Shi Shawara
Ya bayyana nasarorin da gwamnatin ta samu kamar amincewa da mafi ƙanranci da kashi 130% da rage wa’adin sake duba albashi daga shekaru biyar zuwa uku. Ministan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su yi haɗin kai da gwamnati da kuma amfani da damarmamakin da aka samar.
Olawande ya kuma buƙaci a haɗa kai wajen magance rashin aikin yi, yana mai jaddada cewa ba kowa zai iya zama ma’aikacin gwamnati ba. Ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su guji wallafawa ko yaɗa labarun ƙarya a kafafen sada zumunta kuma su nemi yin tattaunawa mai amfani da gwamnati.
Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Tinubu tana sauraron ƙorafinsu kuma tana aiki don samar da mafita.
Shugaban Renewed Hope Ambassadors, Bala Ahmed, ya yi kira da a yi hattara game da wata zanga-zangar da aka shirya. Wakilin tsohon Shugaban Kungiyar ‘Yan Fim na Nijeriya, Zack Orji, ya bayyana haɗarin da zanga-zangar ke tattare da shi, ciki har da tayar da tarzoma da rashin zaman lafiya da cigaban tattalin arziki.