Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Talata, ya yi kira ga kafafen yada labarai da su rika daidaita rahotonninsu.
Ya bukaci masu yada labarai da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na sa ido tare da tallafawa ci gaban kasa.
- Tinubu Masoyin Arewa Ne Ba Kamar Yadda Wasu Ke Juya Maganar Ba – Shettima
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars N2m, Ta Dakatar Da Ɗan Wasanta
Shettima ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar Editocin Nijeriya, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, Mista Stanley Nkwocha, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Talata mai taken ‘Gwamnati, Kafafen Yada Labarai Dole Su Hada Kai Don Ci Gaban Nijeriya – VP Shettima.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp