ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Masoyin Arewa Ne Ba Kamar Yadda Wasu Ke Juya Maganar Ba – Shettima

by El-Zaharadeen Umar
2 years ago
Arewa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibu Masoyin Arewa da ‘yan arewa ne , ba kamar yadda wasu ke juya zance da cewa shi makiyin arewa ne ba.
Sanata Kashin Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi makoncin wasu ‘yan jaridu na arewacin Nijeriya a ofishinsa  da ke  fadar Shugaban Kasa, a Abuja.
  • Zanga-zanga: Gwamnatin Kano Ba za Ta Amince Da Barnata Dukiyar Al’umma Ba
  • Zaben Kananan Hukumomi: Za A Yi Wa ‘Yan Takara Gwajin Kwaya A Kano
Ya kuma  bayyana cewa babu abin da gwamnatin suke buƙata a halin yanzu kamar goyon baya domin su samu damar shimfida ayyukan alheri ga al’ummar Nijeriya.
“Maganar cewa shugaba Bola Tinubu ba ya san mutanen arewa ko addinin Musulmi ba gaskiya ba ne, idan aka duba irin muƙaman da ya ba da a gwamantinsa musamman a manyan ma’aikatu da hukumomin gwamnati.” In ji shi.
Sanata Kashim Shattima ya yi ƙarin haske game da zanga-zangar da wasu matasa suke shirin yi, inda ya bayyana cewa dokar ƙasa ta ba su dama, sai dai ya ce babu wani abu a cikinta da ya wuce koma baya.
A cewarsa, akwai bukatar kafafen yaɗa labarai a wannan lokaci su sanar da al’umma cewa yin zanga-zanga a kan tituna ba zai kawo ci gaba a arewa ba.
“Yau ɗin nan, idan aka ce za a yi wannan zanga-zanga Allah kaɗai ya san irin asarar da za a tafka, duk da cewa ‘yan ƙasa suna da hakkin yin ta, amma matsala wasu marasa kishi na iya canza mata manufa” in ji Shettima.
Ya ƙara da cewa , alƙaluma sun nuna irin yadda shugaban ƙasa ya raba muƙamai a hukumomin ƙasar nan, musamman muhimman wurare da suka haɗa ma’aikatar gona da tsaro da harkar sadarwa da kiwon lafiya da sauransu.
Mataimakin shugaban kasar ya ce wannan gwamnati tana da kyakkyawar tanadi da ta yi wa ‘yan ƙasa domin inganta rayuwar mutanen arewa ta hanyar ɓullo da wasu tsare-tsare don tunkarar matsalar da yankin yake fuskanta.
Sanata Kashin Shettima ya ba da misalin da  ƙirƙirar sabuwar ma’aikatar bunƙasa noma da kiwo, haka na nuna irin yadda shugaba Tunibu ke kaunar arewa, amma wasu na juya labarin da cewa Tunibu makiyin arewa ne.
Kamar yadda Sanata Kashin Shettima ya jefa tambaya inda ya ce wane ne ya sanya hannu a kan dokar hukumar farfaɗo da yankin arewa maso yamma? Kuma wane ne ya kirkiri ma’aikatar bunƙasa noma da kiwo?
Ya ce wannan shugaban ne dai ya amince da a ƙaddamar da tsarin yin amfani da matakin soja da kuma na diplomasiya domin tunkarar matsalar tsaro a arewa maso yamma da zai taimaka wajen warware ta.
Ya ƙara da cewa ta hanyar ɓullo da sabon shirin ECOSYSTEM ga waɗanda iftila’in hare-haren ‘yan bindiga ya shafa, wannan shirin zai inganta rayuwar ‘yan arewa.
Sanata Kashin Shettima ya roki ‘yan jaridu da su haɗa kai su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya wajen samar da ci gaba a arewacin Nijeriya, ya ce wannan gwamnati tana buƙatar addu’o’i a irin wannan lokaci domin samun nasara, amma yanzu ba lokacin zanga-zanga ba ne.
“Mu a nan arewa muna buƙatar  bunƙasa ayyukan ci gaba waɗanda suke da mahimmancin a Nijeriya, saboda haka ba zamu kyale abubuwa su lalace ba” inji shi
Kazalika Sanata Kashin Shettima ya yi kira ga ‘yan jaridu na arewacin Nijeriya da su faɗakar da al’umma irin manyan muƙaman da shugaba Tunibu ya bai wa ‘yan arewa a gwamantinsa domin a bunƙasa ta.
Daga ƙarshe mataimakin shugaban ƙasan ya yi kira ga ‘yan arewa da su goyi bayan gwamnati mai ci yanzu domin a samu cigaba mai ɗorawa.
Arewa
El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Sojoji

Kasurgumin Dan Ta'adda Ya Mika Wuya Ga Sojoji A Borno

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.