Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi jami’an gwamnati da kakkausar murya, cewa duk wanda aka nada shi wani mukami kuma ba zai iya kare mutuncin ofishinsa ba, to ya yi murabus, maimakon ya bata sunan gwamnati.
Gargadin ya biyo bayan murabus din Kwamishinan Sufuri, Ibrahim Namadi Dala, wanda ya sauka daga mukaminsa bayan an alakanta shi da belin wani da ake zargi da laifin safarar kwayoyi.
- Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa
- Sin Ta Samar Da Yuan Biliyan Daya Domin Ayyukan Jin Kai Sakamakon Ibtila’in Ambaliyar Ruwa
Da yake jawabi a taron Majalisar Zartaswa karo na 30 a ranar Laraba, Gwamna Yusuf ya sake nanata cewa, gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin da’a, cin hanci da rashawa, da laifukan da suka shafi muggan kwayoyi ba.
“Bari in yi bayani a fili: ba za mu yarda da duk wata dabi’a wacce za ta ruguza dabi’un da muke tsaye a kai ba. Dole ne kowane jami’in gwamnati ya kasance mai lura da al’amuransa, ba wai kawai ofishin ku kuke wakilta ba, har da mutuncin gwamnati baki daya.” In ji Gwamna Abba Kabir
Gwamna Yusuf, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya jaddada cewa, duk wanda aka samu yana taimakawa ko aikata laifuka to zai fuskanci cikakken fushin doka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp