An wayigari dubban daruruwan jama’ar Kano a yau, na taya juna murnar kubutar da dadadden asibiti mai tarihi a Kano, hada ma daukacin yankin jihohin Arewa bakidaya daga cefanarwa, wato Asibitin Yara Na Hasiya Bayero da ke daura da gidan mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi.
Wasu na danganta taswirar ginin asibitin da shafe Shekaru sama da dari (100) a tsaye, a karkashin kulawar mabanbantan hukumomi, daga bisani, gwargwadon Shekaru talatin (30) da suka gabata ne aka canja akalar wannan dadadden gini mai tarihi zuwa ga wani hamshakin asibiti na yara wanda ba a taba samar da tamkarsa ba a jihar ta Kano tsawon lokaci. Ba a cikin Kano ba kadai, dubban magidanta musammm raunana marasa farcen susa kan yo balaguro daga wasu jihohi da ke makotaka da Kano zuwa ga wannan asibiti na Hasiya Bayero, don neman lafiyar yaransu. Wasu majiyoyi na fadin cewa, wasu mutane kan tsallako hatta daga makotan wannan Kasa tamu ta Nijeriya zuwa ga wannan asibiti da gwamnatin tsohon gwamna Ganduje ta cefanar da shi ga wani dan lelanta, tare da shelanta canja asibitin na yara zuwa wani waje can bayan gari tare da sanya masa sabon suna, wato Asibitin Yara Na Khalifa Sheikh Isyaka Rabi’u, “Khalifa Sheikh Isyaka Rabi’u Paediatric Hospital”.
Duk da irin amfanuwa da dubban talakawa ke yi da Asibitin na Hasiya, sai al’umar Kano suka tashi da mummunan labarin cewa tsohon gwamna Ganduje ya cefanar da shi ga wani hamshakin mutum sananne cikin jam’iya mai mulki ta APC. Masu kimanta wurare, sun kimanta darajar wannan asibiti da kudi naira biliyan shida (N6,000,000,000,00k), amma wani abu mai kama da almara, sai gwamnatin ta Ganduje ta cefanar da wannan asibiti kan kudi naira miliyan shida (N b,000,000,00k) kacal. Duk da irin wannan danyen ciniki, sai naira miliyan guda ne kacal aka samu daga wanda aka saidawa da wannan asibiti da ke rungumar mas’uliyar dubban yara daga ko’ina cikin wannan kasa dare da rana.
A yammacin ranar Talata, 25 ga Watan Yulin 2023, kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Abubakar Yusuf da takwaransa na yada labarai Alhaji Dantiye, suka leka wannan asibiti na Hasiya Bayero, suna masu bibiyar dinbin mazajen miliyoyin kudade da gwamnatin maigirma Abba Kabir Yusuf ta kashe, wajen canja fasalin asibitin kacokan, bayan kwato shi tare da tsarawa gami da nazartar shirye-shiryen bude wannan asibiti nan ba da jimawa ba. A nan ne a gurguje na dan sami damar jin ta-bakin kwamishinan na lafiya game da wannan marayan asibiti da ya tsallake rijiya da baya.
Da farko, na tambayi kwamishinan na lafiya, shin, ko mece ce hikimar dawo wa da al’umar Kano wannan tsohon asibiti nasu, bayan cefanar da shi da tsohuwar gwamnati ta yi? Kwamishina ya amsa ne da cewa, “Saboda shi ne asibiti daya tilo da ke kula da harkar lafiya ta yara zunzurutu, wanda hakkake yawansu wani abu ne mawuyacin gaske. Kuma ga asibitin cikin tsakiyar gari, ko ta ina ne mutumin Kano ya bullo, ba tare da yin wani jibin goshi ba ne zai kai ga asibitin cikin salama. Uwa uba, kusan duk wani abu da ake yi cikin wannan asibiti kyauta ne, sabanin wancan asibitin da suka yi, tare da kokarin mayar da mutane can ko da ba sa so. Cikin wancan asibiti da suka yi, wanda aka dora alhakin tafiyar da shi a hannun wasu mutane ‘yan jari hujja. Abin takaici, duk wani motsi da mutum zai yi cikin wancan asibiti kawai magana ce ta kudi, ko kana da su, ko ba ka da su kai ta shafa.
Komai a asibitin, sai mutum ya biya mazajen kudade tsababa. Kusan a ce, shiga cikin asibitin ne kawai ba za a tare ka a ce ka kawo kudi ba”.
Kwamishina Yusuf ya ci gaba da fadin cewa, “babu shakka tun da aka samar da wannan asibiti, bai sami gatan da ya samu irin wannan lokaci ba. Mun sabunta daukacin kayan aikin asibitin, mun zuba sababbi na zamani; mun zuba gadaje sababbi; mun sanya katifu tuli; mun zuba ababen rufa; mun samar da ababen shimfida su ma sabbi, kai ta wata fuskar ma muna iya cewa hatta ma’aikatan wannan asibiti sabbi ne ful aka samar, abin nufi, mun yi kokarin canja tunaninsu ne, ta yadda za su dukufa yin aiki da gaskiya tare da sanya bukatar jama’a a sama da bukatar kashin-kai, sabanin irin yadda lamura ke gudana gabanin zuwan wannan gwamnati mai albarka ta NNPP.”
Kwamishinan na lafiya ya ci gaba da bayanin cewa, daga wannan lokaci, sun hana yin kyara ko nuna kyamata ga duk wani mutumin da ya zo neman lafiya wannan asibiti da ma sauran daukacin asibitocin da ke a wannan jiha ta Kano. Sannan, kwamishinan, ya nemi babban sakatare mai kula da asibitoci da a hanzarta farfado da tsohon kwamitin da ke karbar korafe-korafen masu zuwa asibiti da ake kira da Sabikom.
A ta bakin kwamishinan, tun wancan lokaci da ya gabata ne suka samar da wannan kwamiti na Sabikom, tare da yin isharar cewa, ta hannun wannan kwamiti ne jama’a za su rika shigar da korafe-korafen nasu, ba tare da yunkurin zuwa saman da har sai an dangane da ofishin kwamishina ba, tun da lamarin zai zamto ne mataki mataki. Hakika gwamnati za ta yi kokarin sharewa jama’ar Kano hawayensu karkashin wannan kwamiti na Sabikom in ji shi.
Har ila yau, kwamishinan ya yi roko ga jama’ar gari, na su taimaka wajen kare irin makudan kudade da aka taskace cikin wannan asibiti, don amfanin jama’ar Kano farko. Sannan, ya yi kira ga wasu kungiyoyi na al’uma da ake kiransu da Abokanan Asibiti, na su taimaki gwamnati wajen sanya idanu wajen ganin ba a sace irin wadannan kayaiyaki na makudan kudade da aka jibge cikin asibitin ba, tare da hana salwantar da kayaiyakin, ko da misali ta hanyar karairaya su ne da makamantansu.
A karshe, na tambayi kwamishinan cewa, har kawo wannan lokaci da muke ciki, akwai wasu asibitoci misali asibitin Kabuga, da za a ga an zaftare wani sashi nasa, tare da mallaka wa wasu mutane shafaffu da mai, ko me zai ce akan haka? Sai ya ka da baki ya ce; “ai za a ga ma’aikata sun je irin wadannan asibitoci sun shafa musu jan fenti, alamar gwamnati ba ta gamsu da abinda aka yi ba ke nan.
Yanzu ma muna dan jiran lokaci ne, amma za mu bibiya, saboda haka gara ma tun da wuri, irin wadannan mutane da suka yi kaka-gida, su hada komatsansu su kauce!
Ko shakka babu kubutar da wannan asibiti ya dawo hannun gwamnati zai yi matukar farfado da harkokin kiwon lafiyar kananan yara ta yadda al’umma za su ci gajiyarsa sosai.