Hukumar lura da harkokin fina-finai ta kasar Sin, ta ce a shekarar 2024 da ta gabata, kudaden shiga da gidajen sinima suka tara ya kai yuan biliyan 42.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 5.91.
Alkaluman baya bayan nan da hukumar ta fitar sun nuna cewa, fina-finan cikin gida na kasar Sin sun samar da kudaden da suka haura yuan biliyan 33.4, adadin da ya kai kaso 78.68 bisa dari na jimillar kudaden shigar. Kaza lika, wasu fina-finai 79 sun samar da kudaden da suka haura yuan miliyan 100, cikin su fina-finai 55 an shirya su ne a cikin gida.
- NAHCON Ta Mayar Wa Alhazan Jihar Kaduna Kudaden Rangwame Na Aikin Hajjin 2023
- Mahaifiyar Tsohon Jarumin Kannywood, Ahmed S Nuhu Ta Rasu
Bugu da kari, a shekara ta 2024, an kara sabbin allunan kallon sinima sama da 4,600 a sassan biranen kasar Sin, kuma da haka jimillar adadin su a kasar Sin ya kai 90,968.
A shekarar 2024, adadin wadanda suka shiga sinimomin kasar ya haura mutum biliyan 1, kamar dai yadda alkaluman suka bayyana. (Saminu Alhassan)