Jimilar kudin ajiyar Sin cikin takardun kudin ketare ta kai dala triliyan 3.3164 zuwa karshen watan Satumba, wanda ya karu da dala biliyan 28.2 ko kuma kaso 0.86 bisa dari, idan aka kwatanta da na karshen watan Agustan bana.
Hukumar kula da kudin musaya ta kasar Sin ce ta bayyana haka a yau Litinin, inda farashin musayar kudin dala ya fadi, kana farashin kadarorin kudi a duniya ya karu a watan da ya gabata.
Ta kara da cewa, tasirin sauyin farashin musaya da na kadarorin ne ya kai ga karuwar kudin ajiyar Sin na ketare a watan Satumba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)