Shugaban Hukumar Fasa Kauri ta Kasa (Kwastam), Kanal Hameed Ali (mai ritaya), ya ce Kamfanin Man Fetur na Nijeriya NNPC, ba zai iya kare matakin yawan makudan kudaden da yake kashewa na tallafin mai a kowacce rana ba, inda hakan ya janyo ake batar da sama da Naira biliyan shida a duk shekara.
Ali ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, a gaban kwamitin majalisar wakilan Nijeriya da ke sauraren bayani kan tsarin kashe kudi daga shekarar 2023 zuwa 2025 na matsakaicin zango.
- 2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?
- Jami’an Kashe Gobara Sun Ceto Mutum 91 Da Dukiyar Da Ta Kai Kusan Naira Miliyan 25 A Kano
Ya kara da cewa babu yadda NNPC zai yi bayanin ikirarin ana amfani da lita miliyan 98 a kowacce rana, inda ya yi zargin kamfanin na kara lita miliyan 38 kan ainahin wanda ake amfani da shi a kowacce ranar.
Kwamitin ya bukaci shugaban hukumar Kwastam din da ya yi bayani kan gibin da aka samu na tsakanin Naira tiriliyan 11 zuwa 12 na kasafin badi.
Gwamnatin Nijeriyar dai ta shigar da bukatar kasafin kudin shekara mai zuwa da ya kai Naira biliyan 19.76, kuma za a samu gibin tsakanin sama da biliyan 11 zuwa sama da biliyan 12.