Kakakin rundunonin soji da ’yan sandan kasar Sin Wu Qian, ya ce kudaden da kasar ke kashewa a harkar tsaro na bisa wani daidaitaccen mataki. Wu Qian ya bayyana haka ne yau Lahadi a wajen taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar.
An bayyana yayin zaman majalisar cewa, daga cikin kudaden da gwamnatin tsakiya za ta kashe a bana, kasafin kudin bangaren tsaro zai kama yuan triliyan 1.78, kwatankwacin dala biliyan 249, karuwar kaso 7.2 kan na bara.
- Dalilin Da Ya Sa Aka Soke Wasan Barcelona Da Osasuna
- Hadin Kai Ne Kadai Zai Kai Masana’antar Kannywood Tudun Mun Tsira -Ado Ahmed Gidan Dabino
Idan aka kwatanta da kasashe masu karfin soji kamar Amurka, abun da Sin take kashewa a bangaren bai taka kara ya karya ba, idan aka yi la’akari da GDPnta, da kudaden da take kashewa, da abun da take kashewa kan tsaron kowanne mutum, da ma kan kowanne jami’in tsaro.
Kakakin ya jaddada cewa, har yanzu kasar Sin ba ta kai ga dunkule yankuna wuri guda ba, kuma tana fuskantar barazanar tsaro cikin yankinta, wanda ke cikin mafiya sarkakiya a duniya.
Wu Qian ya nanata cewa, makaman Amurka da dama, ba za su taba hana murkushe ’yancin Taiwan ba. Kuma dunkulewar yankunan Sin wuri guda shi ne abu mafi tasiri, yana mai cewa ba karfi ne kadai ke ingiza hakan, har da muradin al’umma. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp