A jiya Laraba ne kudirin doka da ke neman samar da kafar tsarin bayar da tallafin kudi karatu ga dalibai ‘yan Nijeriya ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawan Kasar.
Kudurin dokar da Sanata Umar Sulieman (APC, Kwara ta Arewa) ya kawo, na neman samar da sahihin tsari don samun nasarar samar da kudaden tallafin karatu ga Dalibai.
Suleiman, a muhawarar da ya jagoranta kan ka’idojin kudirin, ya ce tsari za a tanada Irin yadda ake tanadar da tsarin gudanar da mulki ko shugabanci.
A cewarsa, Shirin Taimakon Kudade na Dalibai na Kasa, bayan ya Samu karbuwa, daliban za su ci gajiyar ne ba tare da biyan karin kudin ruwa ba.
Ya kuma kara da cewa, kafa wannan tsarin zai bai wa daliban da suka cancanta a manyan Makarantu damar samun lamunin wanda babu ruwa acikin shi.