Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce akwai bukatar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi garambawul a tsarinsa domin tabbatar da ci gaba da dacewarsa a harkokin duniya.
Shugaban, wanda ya nanata shirye-shiryen da NIjeriya ke da ita na wakiltar Afirka a cikin Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira ga shugabannin kungiyar G20 da su amince Nahiyar Afirka ta samu kujeran dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.
- Tsarabar Taron Kolin G20
- Jami’in Yada Labarai: Kasar Sin A Shirye Take Ta Aiwatar Da Hadin Gwiwar Kasashe Na Hakika Tare Da Mambobin G20
Ya yi wannan rokon ne a taron koli na shugabannin kungiyar G20 karo na 19 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.
Shugaba Tinubu ya ce, “Ya kamata kwamitin tsaro ya fadada rukunin mambobi na dindindin da wadanda ba na dindindin ba don nuna bambance-bambancen duniya da yawan jama’a, domin Afirka ta cancanci a ba ta kujeran dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.
“Afirka ta cancanci fifiko a wannan tsari, kuma ya kamata a ba ta kujeru biyu na dindindin tare da daidaita matsayinta. A sherye Nijeriya take ta zama wakiliyar Afirka a wannan matsayi.”
Sanarwar ta shugaban wadda Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar ya karanta a madadinsa, ta yi nuni da cewa, kungiyar G20 a halin yanzu tana sanye da wani tsari na cibiyoyi na kasa da kasa masu sa ido da ke goyon bayan ra’ayin sauye-sauye a bangarori da yawa.
Ya kuma yaba wa matakin da G20 ta dauka na bai wa kungiyar tarayyar Afirka damar zama mamba ta dindindin da kuma yadda take gayyatar kasashen da za su shiga kungiyar.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba da kafa kungiyar kawance na yaki da yunwa da kuma fatara, wanda Shugaban kasar Brazil, Luiz Lula da Silba ke jagoranta, yana mai cewa kawancen na da matukar muhimmanci wajen yaki da yunwa da fatara a duniya.
Sannan ya yaba da shirin tare da bayyana shi a matsayin matakin da ya dace don magance daya daga cikin manyan kalubalen duniya.
Shugaba Tinubu ya kwatanta wannan shiri na duniya da daya daga cikin fannoni takwas da ya zayyana a bikin rantsar da shi watanni 18 da suka gabata, inda ya bayyana aniyar Nijeriya na daukar kyawawan halaye na kasa da kasa don ciyar da tattalin arzikinta gaba.