Kwanan nan, kasar Sin ta harba kumbon Shenzhou-14 mai dauke da ’yan saman jannati cikin nasara, kuma daga bisani ’yan saman jannatin guda uku da ke cikin kumbon sun shiga babban sashen Tianhe na tashar sararin samaniya ta kasar kamar yadda aka tsara.
Abin lura a nan shi ne, cikin tsawon watanni shida da ’yan saman jannatin za su shafe suna gudanar da aiki a wannan karo, ana sa ran za su kammala gina tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, matakin da ke nuna cewa, bayan da masu nazarin sararin samaniya na kasar Sin suka shafe tsawon shekaru 30 suna kokari ba tare da kasala ba, za su cimma burinsu.
A yayin da kasar Sin ke kokarin cimma burinta game da binciken sararin samaniya, kullum kofarta a bude take ga ragowar kasa da kasa wajen gudanar da hadin gwiwa.
Kawo yanzu, tana gudanar da hadin gwiwa da kasashe da dama a wannan fanni, wadanda suke gudanar da gwaje-gwajen kimiyya a tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin. Nan ba da jimawa ba, ana sa ran ’yan saman jannati na wasu kasashe ma za su shiga tashar ta kasar Sin.
Ma iya cewa, nasarar harba kumbon “Shenzhou-14” ba nasarar ce ga kasar Sin kadai ba, babban ci gaba ne ga dan Adam baki daya wajen cimma burinsu na bai daya game da aikin binciken sararin samaniya. (Mai zane: Mustapha Bulama)