Naurar tashi ta kumbon binciken duniyar wata ta kasar Sin wato Change-6, ta tashi daga doron duniyar wata da safiyar yau Talata, dauke da samfuran da ta tattaro daga yanki mai nisa na duniyar watan, lamarin da ya kasance wani gagarumin nasara a tarihin dan adam na binciken duniyar wata.
Hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta ce naurar ta shiga falakin da aka tsara a zagayen wata.
An harba kumbon Changee-6 da ya kunshi naurorin zagaye da ta sauka da tashi da ta dawowa, kamar magabacinsa Change-5, a ranar 3 ga watan Mayu. A kuma ranar 2 ga wata ne naurar tashi da sauka ta kumbon, ta sauka a yankin gulbin dake kudancin duniyar wata da ake kira South Pole-Aitken Basin.
Kumbon Change6 ya kammala ayyukansa masu fasaha da tattara samfura, kuma kamar yadda aka tsara, samfuran na cikin wani mazubi dake cikin naurar tashi dake jikinsa. (Mai fassara: Faiza Mustapha)