Kungiyar Yobe First Movement (YFM), mai gudanar da ayyukan jin-kai da tallafa wa al’umma, ta bai wa marayu tallafin atamfofi 400 tare da shaddodi 100, da ke fadin jihar Yobe.
A sa’ilin da yake karbar kayan tallafin, shugaban kungiyar direbobi ta Nijeriya (NURTW), reshen jihar Yobe, Karimi Alhaji Goni, ya bayyana matikar jindadi dangane da tallafin, inda ya ce hakan zai taimaki marayun, wadanda mafi akasari, iyayensu sun rasu ne ta dalilin haduran kan hanyoyi.
- Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Tattauna Da Wakiliyar CMG
- Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Tattauna Da Wakiliyar CMG
“Wannan shi ne karon farko wanda wata kungiya ta tuna damuwa tare da tallafa wa marayun mu, kimanin 700. Allah ya saka wa YFM da alheri, bisa ga wannan tallafin da ta bai wa marayun mu.
“Muna kira ga sauran kungiyoyi, ‘yan siyasa, masu hannu da shuni tare da gwamnatoci, cewa kofarmu a bude take wajen neman taimakon kayan abinci, tufafi da makamantan su.” In ji Goni
Alhaji Goni ya kara da cewa, gungiyar su ta direbobi, ta na da mambobin sama da 30,000 a fadin jihar Yobe. Ya ce, kullum suna kan hanya, yau ace wannan ya yi hadari ya karye, gobe wannan ya rasu.
“Saboda haka mu na rokon gwamnatin jihar Yobe tare da Hukumar Sake Raya Arewa Masu Gabas da sauran kungiyoyi, su kawo wa marayun mu daukin gaggawa.” In ji shi.
A nashi bangaren, Kodinatan YFM a jihar Yobe, Malam Sadiq Muhammad ya ce, sun zabi bai wa marayun wannan tallafin, ta hanyar la’akari da halin da ake ciki na matsin rayuwa.
Ya ce, “Abubuwan da muka bayar tallafi ga marayun, a karkashin kungiyar direbobi ta NURTW, daga kananan hukumomi 17 dake fadin jihar Yobe, sun kunshi turamen atamfofi 400 ga yara mata, da shaddodi 100 ga yara maza, da Naira 100,000 don biya musu kudin mota zuwa garuruwan su.” In ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp