A ranan Asabar da ta gabata ce, kungiyar agaji karkashin jagorancin Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta zabi sabbin shugabbaninta na Jihar Kogi.
Bikin wadda ya samu halartan mambobin kungiyar daga dukkan kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar ya gudana ne a sakatariyar kungiyar Jama’atu Islam (JNI) da ke garin Lakwaja, Babban Birnin Jihar Kogi.
- Ko Makiyan Buhari Sun San Aikin Da Ya Yi Yafi Na Gwamnatocin Baya -Minista
- Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya
Shugabannin da suka sha rantsuwa sun hada da Alhaji Suleiman Yusuf Ibadurahman (Shugaba), Mallam Haruna Nalado (Mataimakin Shugaba), Alhaji Abbas MG (Sakatare), Abdulkarim A Alao (Darakta), Shafiyi Saminu (Ma’aji), Abdullahi Usman (Jami’in kula da aikin Hajji), Muhammed Jami’u (Sakataren Kudi), Ibrahim T Musa (Mai Kididdigar Kudi) da kuma Tanimu Muhammed (Sakataren Shirye-shirye).
Sauran su ne, Ibrahim Muhammed (Jami’i mai kula da aikace-aikace), Ahmed Ibrahim (Jami’in hulda da Jama’a na Biyu), Muhammed Usman Sarki (Mataimakin jami’in kula da aikin Hajji), Zakariya Adam (Mataimakin jami’in magance bala’o’i), Hassan Ahmadu, Jibril Haruna da kuma Idris Usman.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp