Kungiyar ta APOSUN wacce aka fi sani da POS da ke sana’ar hada-hadar kudi na tafi da gidanka a Nijeriya, ta shugaban ‘Yansandan Kasar nan.
Kungiyar ta ce wannan na cikin ziyarce-ziyarcen da take kan aiwatarwa tun daga shekarar 2022 da ta gabata, domin ganin ta hada hannu da hukumomin tsaron Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren kudi ta yadda za a kau da bara-gurbi da ke amfani da na’urar POS wajen aikata masha’a.
Kungiyar ta Association Of Poit Sale Users In Nigeria mai inkiya da APOSUN ta jaddada aniyarta na yin aiki da rudunar ‘yansandan kasar nan.
Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyat Barista Abdullahi Gurin, ya ce mambobin Kungiyar a shirye suke da su hada hannu da duk wata hukuma ta gwamnati ko ma cibiya mai zaman kanta domin tsaftace sana’ar ta POS, haka ne ma ta sa suka nemi zama da rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
“Mun rubuta wa Sufeto Janar din ‘yansandan Nijeriya kan cewa masu hada-hadar kudi, don haka muka ziyarce shi don mu fada masa abubuwan da Kungiyar nan ke ce ciki,”
“Hukumar ‘Yansanda sun bamu tabbacin cewa duk matsalolin da za mu fuskanta suna bayanmu, sannan kuma suna goyon bayanmu a kan ayyukan da muke yi, kuma sun bamu tabbacin duk jihar da muke da matsala mu shiga kai tsaye kawai wajen Kwamishina na wannan jihar ko DPO mu fada matsalolinmu za su magance mana ba tare da bata lokaci ba,” in ji shi.
A nasa bangaren Sakataren Tsare-tsare a Matakin Kasa na APOSUN Alhaji Alhaji Maina Abdullahi, ya bayyana cewa tabbatar da duk wasu bayanai kan yadda ayyukan Kungiyar ke gudana ya kai ga daukacin mambobinsu, wanda a cewarsa a yanzu haka Kungiyar na da rassa a jihohin Nijeriya 36 har da Abuja da kuma Kananan hukumomin Kasar 774.