Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi kira ga mahukuntan Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da su soke jarrabawar da ake yi a makarantar har sai an dakatar da yajin aikin da kungiyar ke yi a kasar nan.
A cewar ASUU, dole ne a sake gudanar da jarrabawar lokacin da kungiyar ta janye yajin aikinta.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa hukumar gudanarwar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta sake bude jami’ar yayin da reshen ASUU na Jami’ar ya bijirewa Barazanar Gwamnan jihar, inda Malaman suka tsaya kai da Kafa cewa har yanzun yajin aikin na ci gaba da tafiya.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan kungiyar ASUU na shiyyar Kano, Kwamared Abdulkadir Muhammad, ya bayyana cewa idan har mahukuntan jami’ar suka gaza soke jarabawar, kungiyar za ta kasance ba ta da wani zabi illa rubuta takardar koke ga hukumar jami’o’in ta kasa (NUC) da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC).