Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel ya ce an ”martaba shi” da ya samu damar bayar da gudunmuwa a kungiyar, kuma ba zai manta rawar da ya taka a kungiyar ba har abada.
A satin da ya gabata ne Chelsea ta kori Tuchel, mai shekara 49, bayan da ya ja ragamar kungiyar wasanni sama da 100, bayan da ya yi rashin nasara a gidan kungiyar Dinamo Zagreb a gasar cin kofin zakarun turai da ci 1-0 a wasan farko na cikin rukuni.
Chelsea ta nada kociyan kungiyar Brighton Hobe Albion, Graham Potter, domin ya ci gaba da horar da kungiyar, wanda ya amince da fam miliyan 21 tare da tawagarsa ta masu taimaka masa.
Mai koyarwa Tuchel ya ce ya ”kadu” da jin labarin cewa an kore shi daga aikinsa sannan tsohon kociyan na Borussia Dortmund da Paris St-Germain ya bar Stamford Bridge, bayan ya lashe kofuna uku a watanni 20 da ya ja ragamar kungiyar inda ya lashe gasar cin kofin zakarun turai na Champions League a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 a kakar farko da ya ja ragamar Chelsea.
Chelsea wadda ta sanar da korar Tuchel ta kara da cewar, sabon wanda ya mallaki kungiyar, Todd Bohley ya gamsu cewar ta sallami kocin a lokacin da ya dace domin yana fatan gina sabuwar Chelsea.
”Wannan kungiya ce da nake jin tamkar gida ce a waje na ina godiya ga dukkan wadanda suka taimaka min gudanar da aiki da ‘yan wasa da magoya baya, wadanda kullum suke min tarbar girma tun daga ranar farko” In ji Tuchel.
Ya kara da cewa ”Farin ciki na da alfaharin da na taimaka kungiyar ta lashe Champions League da kuma Club World Cup ba zai taba gushewa ba a rayuwata domin martaba ce da na samu damar bayar da gudunmuwa a kungiyar, ba zan manta da sama da watanni 19 da na yi aiki a kungiyar ba, zan ci gaba da tunawa a rayuwata.
Chelsea tana ta shida a teburin gasar Premier League, bayan cin wasanni uku da canjaras daya da shan kashi a wasa daya kuma sabon wanda ya sayi Chelsea ya kashe fam miliyan £255, wajen sayo sababbin ‘yan wasa, kungiyar ta kafa tarihin kashe kudi a kaka daya wajen cefane.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp