Wakilan Kungiyar Haɗin Kan Musulunci ta Duniya Sun Ziyarci Madina Baye Niass da ke Kaulakha a Ƙasar Senigal.
Talla
Tawagar Ƙungiyar Haɗin Kan Musuluncin ta Duniya dai ta kai ziyarar ce bisa jagorancin Babban Sakatarenta, Dakta Abdurrahman Ibn Abdallah zuwa Medina Baye Niass.
![Niass Niass](https://hausa.leadership.ng/wp-content/uploads/2022/08/FB_IMG_1660809099340-300x168.jpg)
Ziyarar dai ta musamman ce domin rattaba hannu na haɗin gwiwa a tsakanin Kungiyar Musuluncin ta Duniya da Ƙungiyar Haɗin Kan Musulmi ta Afirka da aka ƙaddamar kwanan baya a Ƙasar Sudan wadda aka damƙa shugabancinta a hannun Khalifan Shehu Ibrahim Niass, Shehu Muhammadul Mahi Niass.
Talla