A ranar Alhamis ce, Kungiyar NURTW ta kasa bangaren ‘J5 container’ reshan Jihar Legas a shiyar kasuwar Mile12 Intanashinal maket karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Umar Ahmed Isah ta gudanar da taron neman hadin kan jami’an tsaro na bangarori daban-daban na cikin garin Legas.
Kungiyar ta hada kai ne da bangarorin jami’an tsaro da suka hada da hukumar Kwaston da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da hukumar kula da hanyoyi da hukumar ‘yansanda da dai sauransu.
- Tinubu Ya Isa Legas Don Gudanar Da Bukukuwan Kirsimeti Da Sabuwar Shekara
- Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Legas Za Ta Kara Samar Da Kwararru – Kwamishina
Taron neman hadin kan jami’an tsaron ya samu halartar dukkan wakilan kungiyar na kananan hukumomin Jihar Legas da shugabanta na wasu jihohin arewacin Nijeriya, wanda suka hada da shugaban kungiyar na Kaduna, Suleman Muhammad Kaduna da shugaban kungiyar na Kano, Muhammad Sani Kano da shugaban kungiyar na Katsina, Idiris Umar Katsina da shugaban kungiyar na Filato, Kwamared Isah Filato da shugaban kungiyar Narto na Filato, Buhari Bulama.
Sauran sun hada da shugaban kungiyar na Bauchi, Buhari Suleman Bauchi da shugaban kungiyar na Borno, Ahmed Muhammad Barno da shugaban kungiyar Nato a Abuja, Umar Sarki da shugaban kungiyar na Kafanchan, Maiwada Musa da ko’odinetan kungiyar a Jos, Salisu Adamu da sauran shugaban kasuwar Mile12 Intanashinal maket, Alhaji shehu Usman Jibirin.
Makasudin gudanar da wannan shi ne, neman hadin kan jami’an tsaro da kuma jaddada dankon zumunci a tsakaninsu tare da kara fahimtar juna baki daya, a yayin da jami’an tsaron na kowanne bangare suka gabatar da jawabansu daya bayan daya tare da jawo hankulan direbobin da su daina shan kwayoyi da kuma rage yin gudu a lokacin da suke tuki, domin kare lafiyarsu da rayuwar fasinjojinsu.
Haka kuma sun shawarci direbobin J5 container da sauran direbobi masu daukar kaya daga Legas zuwa arewacin Nijeriya da su rika tantance kayan da za su dauka kafin a loda masu a motocinsu, domin kauce wa daukar haramtaccen kayan da gwamnati ba ta yarda da shi ba.
Shugaban kungiyar J5 container da ke shiyar kasuwar Mile 12, Alhaji Umar Ahmed Isah ya yi jawabin godiya ga shugaban kungiyar na kasa da wakilanta na jihohi dangane da irin gudummawar da suke bai wa kungiyar NURTW tun daga sama har zuwa kasa.