Kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar Sin CSHRS, ta fitar da wani rahoton da ya bankado jerin laifuffukan take hakkokin bil Adama da kasar Amurka ta aikata a yankin Gabas ta Tsakiya da kewayensa, wadanda kuma suka yi matukar sabawa dokokin kasa da kasa.
Rahoton da kungiyar ta fitar a jiya, mai taken “Amurka ta aikata laifuffukan take hakkokin bil Adama a Gabas ta Tsakiya da kewayensa”, ya mayar da hankali ne kan yadda Amurkar ta keta hakkokin bil Adama da suka hada da kaddamar da yake-yake, da yi wa fararen hula kisan kiyashi, da lalata hakkokin jama’a na rayuwa da tilasta sauyin rayuwa, da kakaba takunkumai, da keta hakkokin al’umma na samun ci gaba da na rayuwa da na kiwon lafiya, wadanda suka haifar da rikici tsakanin fararen hula da tsananta garkame mutane, da azabtar da su da take ‘yancin bin addini da mutuncin jama’a.
Rahoton ya jaddada cewa, Amurka ta aikata laifukan yaki da cin zarafi da tsare mutane ba bisa ka’ida ba da yi wa fursunoni gwale-gwale da yin gaban kanta wajen kakaba takunkumai na ba gaira ba dalili, a yankin Gabas ta Tsakiya da kewayensa.
Ya kara da cewa, shaidu sun nuna cewa, Amurka ta yi tsananin keta hakkokin bil Adama a yankin Gabas ta Tsakiya da sauran wasu wurare, lamarin da ya haifar da illa da asara ta dindindin ga kasashen da al’ummominsu.
A cewar kungiyar, yayin da aka bankado dabi’un Amurka na danniya da mugunta da keta, da mummunan tasirin karfinta na siyasa, mutane a fadin duniya za su kara fahimtar munafurci da yaudara irin na demokuradiyyar Amurka da yanayinta na kare hakkokin jama’a. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp