A daren Laraba ne majalisar zartaswa ta Kungiyar kwadago ta Nijeriya da kuma TUC suka yanke shawarar dakatar da yajin aikin sai baba-ta-gani da suke yi a fadin kasar.
Kungiyar ta ce, dakatarwar ta biyo bayan shiga tsakani da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya yi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, duka cibiyoyin kwadagon sun umurci mambobinsu da kungiyoyin da suke da alaka da su da su fara yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, 2023 kan cin zarafin shugaban NLC, Joe Ajaero, da ‘yansanda suka yi a Owerri, jihar Imo, a ranar 1 ga watan Nuwamba.
Cikakken labarai na zuwa daga baya…