Gamayyar Kungiyoyin Mata a karkashin inuwar Kungiyar mata da ke fafutukar ganin an samar da shugabanci nagari a kasar nan, wato ‘Women Link For Better Gobernance’, sun yi wa shugabanin kungiyoyin mata bita domin su janyo hankalinsu a kan zaben 2023, mussaman matan Arewacin kasar kan su fito su jefa kuri’un su ga ‘yan takarar da suka cancanta a zabe mai zuwa.
A hirarta da LEADERSHIP Hausa ta yi da Mataimakiyar Shugabar gamayyar kungiyoyin kuma shugabar kungiyar da ke koyar wa mata sana’o’in hannu, Hajiya Aisha Gambo jim kadan bayan kammala taron da ya gudana a Jihar Kaduna ta bayyana cewa, “Makasudin shirya wannan taron shi ne, domin mu wayar wa mata ‘yan’uwanmu kai, musamman matan da ke a arewacin kasar nan, ganin cewa mune a kan gaba wajen fita kwanmu da kwarkwata domin jefa kuri’u a lokacin zabe, amma kuma da an ci zabe sai a barin mu a baya ba tare da an inganta rayuwarmu ba.
“Mun wayar wa shugabanin kungiyoyin mata da ke a Jihar Kaduna kai kusan sama da 200, bisa nufin in son koma gida, su ma za su tara sauran ‘ya’yan kungiyoyin mata da suke jagoranta don su wayar masu da kai kan mahimmancin fitowar jefa kuri’un ga ‘yan takarar da suka cancanta lokacin zaben.
“Mata da dama sun yi fishi kan yadda wasu ‘yan siyasar da aka zaba a baya ba su inganta rayuwarsu, inda hakan ya sa matan suka ce sun daina fita jefa kuri’a. Shi ya sa muka hada kai domin mu wayar masu da kai da yi masu nasiha a kan mu yi hakuri mu fito mu jefa kuri’unmu ga ‘yan takarar da suka cancanta.
“Nan ba da dade wa ba, za mu sake wani sabon gangamin wayar da kan ‘yan’uwanmu mata kai wadanda za su fito daga kananan hukumomin 23 da ke a cikin jihar Kaduna kan muhimmancin jefa kuri’a a zaben 2023.”
Ta kuma yi kira ga iyayen da ke fadin kasar nan da su ja hankalin ‘ya’yansu kar su bari a yi amfani da su don yin bangar siyasa a zaben 2023.
Ita kuwa shugabar gamayyar kungiyar matan, Hajiya Maryan Yahaya Sani wacce kuma ita ce Shugabantar Gidauniyar Ummulkhairi ta ce, “Yanzu mu mata muna son mu hadu mu kafa gwamnati wacce za ta kare martabarmu da kuma ‘ya’yanmu”.