Wata ƙungiya ta gamayyar ƙungiyoyin rajin kare dimokuraɗiyya da haƙƙin dan Adam, CSAGP, sun gudanar da zanga-zanga a hanyar shiga harabar Majalisar Dattawa, inda suke neman a cire Ƙaramin Ministan Tsaro, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle.
Masu zanga-zangar na so a cire Matawalle ne sabida zarginsa da Gwamnatin Zamfara ta yi kan harƙallar “sace kuɗaɗe da batun matsalar ‘yan bindiga a jihar.”
- Majalisa Ta Soke Bukatar Siyo Jirgin Ruwan Shugaban Kasa, Ta Kara Kudin Ga Lamunin Dalibai
- Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Da Kafa Kamfanin Abinci Na ‘Arla’
An ga masu zanga-zangar a hanyar zuwa Majalisar Ƙasa dauke da kwalaye da alluna da rubutu akai a ranar Talata, suna kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya nusar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, domin ya tsige Matawalle.
Masu zanga-zangar waɗanda ake kiran gamayyar ƙungiyar ta su da suna ‘Civil Society Advocacy Groups and Probity’, sun kuma zargi Minista Matawalle da laifin jawo ‘yan bindiga a jiki, lamarin da suka ce ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da dama a Zamfara da asarar dukiyoyi na Biliyoyin Nairori.
Gungun gamayyar ƙungiyar a ƙarƙashin Danesi Momoh, a wani taron manema labarai a ranar Lahadi ya yi kira da a sauke Karamin Ministan Harkokin Tsaron tun a baya.
‘Yan watanni kaɗan kafin saukarsa daga kan kujerar Gwamnatin Zamfara a ranar 29 ga Mayu, EFCC ta zargi Matawalle da karkatar da Naira biliyan 70 na al’ummar jihar, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakaninsa da shugaban EFCC na lokacin, Abdulrasheed Bawa.
Masu zanga-zangar sun damƙa wa Majalisar Dattawa takardar ƙorafi domin isarwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio, mai ɗauke da zargin cewa, mutum kamar Matawalle ba abin bai wa amanar tsaron ƙasa ba ne, musamman muƙami mai muhimmanci a Ma’aikatar Harkokin Tsaro.
Sun kafa hujjojinsu da dalilansu kan wasu zarge-zargen da Gwamantin Zamfara ta watsa kuma ta wallafa, mai nuni kan yadda Matawalle ya karkatar da Biliyoyin Nairorin Zamfara, a harƙallar kwangiloli daban-daban, ciki har da kwangilar gina filin jirgin saman saukale da lodin kaya a Gusau.