A game da batun bikin cika shekaru 60 da kafuwar yankin Xizang mai cin gashin kansa na kasar Sin, wani bincike da CGTN ta gudanar a duniya tsakanin masu bayyana ra’ayoyi 6,747 daga kasashe 38, ya nuna cewa, baki dayan wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun yaba da ci gaban da aka samu a duk fadin yankin Xizang ta fuskar bunkasar tattalin arziki da walwalar jama’a, tare da yabawa da sabon sauyin da aka samu ta hanyar sauye-sauyen dimokuradiyya.
Binciken ya kuma nuna cewa, kashi 74.8 cikin dari na wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun amince da cewa, zamanantarwa irin ta Sin ce kashin bayan ci gaba mai kwari da yankin Xizang ya samu.
CGTN da Jami’ar Renmin ta kasar Sin ne suka gudanar da wannan bincike ta hannun cibiyar sadarwa ta duniya a sabon zamani. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp