“Bunkasuwar gama gari na kasuwanni masu tasowa da kasashe masu tasowa wanda BRICS ke wakilta yana matukar canza yanayin duniya.” Kamar yadda shugaba kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, “Ko wace irin cika za a samu, BRICS wanda ya kasance karfi mai inganci da kwanciyar hankali, zai ci gaba da bunkasa.” Wani bincike da kafar CGTN ta gudanar tare da hadin gwiwar jami’ar Renmin ta kasar Sin, da kuma cibiyar sadarwa ta kasa da kasa ta New Era, ga masu bayyana ra’ayoyinsu 1,634 daga kasashen BRICS, ya nuna cewa, yawancin wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, karfin ikon BRICS ya kara kuzari ga yadda ake gudanar da harkokin duniya. Kana yana da matukar muhimmanci na inganta gina tsari kasa da kasa mai kyau da ma’ana.
A duniyarmu ta yau, dunkulewar tattalin arzikin duniya na fuskantar kalubale, inda ake samun rashin jituwa tsakanin hadin gwiwar bangarori daban daban da masu daukar matakai bisa radin kai, da kuma rashin jituwa tsakanin adalci da danniya da mamaya. Tazarar ci gaba tsakanin kasashe masu ci gaba da masu tasowa na ci gaba da fadada. Halin hukumomi da kuma sabani mai zurfi na tsarin kasa da kasa da wasu tsirarun kasashen da suka ci gaba suka mamaye suna kara fitowa fili. Babban burin kasashen BRICS shi ne su sa kaimi ga gina sabon tsari na kasa da kasa wanda ya fi dacewa kuma mafi adalci.
A cikin binciken, kashi 96.2 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, ya kamata kasashe su shiga cikin harkokin kasa da kasa a dama da su, su hada kai don kafa tsari na kasa da kasa. Kashi 72.6 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun goyi bayan sauye-sauyen da suka wajaba ga dokokin kasa da kasa na yanzu, wadanda kasashen da suka ci gaba suka mamaye. Bugu da kari, wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu na BRICS suna da kyakkyawan fata ga Majalisar Dinkin Duniya a matsayin tushen tsarin kasa da kasa. Yayin da kashi 83.9 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu suka yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kara mai da hankali kan bukatu da bukatun kasashen masu tasowa. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)