A lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalar sauyin yanayi, idanun duniya na kan Dubai. A yau ne aka bude babban taron kasashen da suka rattaba hannu kan tsarin sauyin yanayi na MDD karo na 28 Ko COP28. Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta yanar gizo na baya-bayan nan da CGTN ta gudanar ya nuna cewa, kashi 90.3 cikin dari na wadanda da suka kada kuri’a sun yi imanin cewa, babu wata kasa da za ta kubuta daga matsalar sauyin yanayi, kuma ra’ayin bangarori daban-daban shi ne hanyar magance matsalar sauyin yanayi. Bugu da kari, kashi 91.4 cikin dari na wadanda suka kada kuri’a sun yaba da gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen sa kaimi ga inganta harkokin da suka shafi yanayin duniya.
An fitar da binciken ne a kafafen yada labarai na CGTN da harsunan Turanci da Sipaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 10512 suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Mai fassara: Yahaya)