An shirya cimma ainihin burin ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na wannan shekara cikin nasara. Sakon da aka fitar a muhimmin taron tattalin arziki na shekara-shekara na kasar Sin ya kasance tamkar “harbi a hannu” ga tattalin arzikin duniya dake tangal-tangal. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta yanar gizo da kafar CGTN ta gudanar ta nuna cewa, kashi 92.4 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu na da kwarin gwiwa game da yanayin tattalin arzikin kasar Sin, suna fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a matsayin jigon bunkasar tattalin arzikin duniya da kuma ba da tabbaci ga tattalin arzikin duniya. Duk da koma bayan da aka samu a tattalin arzikin duniya, bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da kasancewa cikin sahun gaba na manyan kasashe masu karfin tattalin arziki. Dangane da haka, kashi 89.4 bisa 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, wannan ya isa ya tabbatar da cewa, farfadowar tattalin arzikin duniya ba zai yi nasara ba, ba tare da ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba, yayin da kashi 87.2 cikin 100 ke son cin gajiyar bude kofar da Sin ta yi ga kasashen waje, da more damarmakin ci gaban kasar Sin. Dangane da yanayin karuwar kariyar cinikayya, kasar Sin ta himmatu wajen inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, tare da tabbatar da cewa an raba moriyar ci gaba tsakanin dukkan kasashe yadda ya kamata. Tun daga wannan watan, kasar Sin ta soke haraji kan dukkan kayayyakin dake shigowa daga kasashe mafi karancin ci gaba da suke huldar jakadanci da su. A cikin binciken, kashi 91.9 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da ayyukan da kasar Sin ta aiwatar wajen inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, suna ganin cewa, wannan shiri ya ba da muhimmiyar gudummawa wajen raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen duniya masu tasowa, kana ya bayyana kokarin kasar Sin a matsayin babbar kasa mai iko, da kuma aniyarta ta karfafa hadin gwiwar kasa da kasa.
An fitar da sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’ar a kafar CGTN cikin harsunan Turanci da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda sama da mutane masu amfani da yanar gizo 5,142 suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Mohammed Yahaya)