Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila.
Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Kashi 81.8 cikin 100 kuma sun bayyana cewa, “kafa kasa mai cin gashin kanta, mai cikakken ‘yanci ta Falasdinu bisa kan iyakokin da aka shata a shekarar 1967, tare da gabashin Kudus a matsayin babban birninta” ta zama wata matsaya da aka cimma a tsakanin kasashen duniya.
A cewar bayanai daga hukumomin kiwon lafiya na Gaza, hare-haren sojojin Isra’ila a Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane 65,283 tare da jikkata wasu 166,575 tun bayan sabon rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da Falasdinu a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2023. A kuri’ar jin ra’ayoyin, kashi 90.8 cikin 100 na wadanda suka yi Allah-wadai da ta’asar da Isra’ila ke tafkawa, kuma sun yi imanin cewa, ya kamata Isra’ila ta gaggauta dakatar da hare-harenta na soji a zirin Gaza. Kazalika, kashi 92.1 cikin 100 sun yi kira ga kasashen duniya da su dauki mataki tare da yin taron dangi wajen taka birki ga farmakin sojojin Isra’ila a Gaza. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp