Bayan shafe lokaci ana mahawara a zauren majalisar dattijan Amurka, kudurin cikakkiyar dokar rage haraji da kashe kudaden gwamnatin kasar ya samu wucewa da kyar, kudurin dokar da ya yi matukar samun goyon bayan shugaban kasar Donald Trump.
Kafin hakan, sai da mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya jefa kuriar raba gardama, wanda hakan ke nuni ga zurfin rabuwar kai tsakanin alummun Amurka, tare da fadada damuwar sassan kasa da kasa kan lamarin.
- Ɗan Wasan Liverpool, Diogo Jota, Ya Mutu A Hatsarin Mota
- Sin Ta Bai Wa Habasha Kayayyakin Tallafin Jinya
Sakamakon wata kuriar jin raayin jamaa ta yanar gizo da kafar CGTN ta kasar Sin ta fitar, ya nuna kaso 89.1 bisa dari na masu bayyana raayoyinsu na ganin kudurin dokar mai lakabin “big and beautiful” bill, ya dada fito da yanayi na karo-da-juna dake tattare da dimokaradiyyar Amurka, kuma kudurin dokar ba zai sake bunkasa Amurkar ba.
Kudurin dokar dai na da nufin rage kudaden da gwamnatin kasar za ta kashe a fannin tallafin kiwon lafiya da kusan dalar Amurka biliyan 600 cikin kusan shekaru 10, da rage adadin masu cin gajiya daga tallafin kiwon lafiya da kusan mutum miliyan 11, tare da kara adadin kudaden kashewa a wasu manyan fannoni ga karin wasu mutum miliyan 24.
Game da hakan, kaso kusan 88.2 bisa dari na masu bayyana raayoyinsu sun soki kudurin, wanda suka ce zai gurgunta tsarin kiwon lafiyar Amurka, tare da gargadin zai haifar da koma baya ga ingancin lafiyar Amurkawa. Har ila yau, kudurin rage harajin ana hasashen zai fadada gibin kudaden kashewa na gwamnatin Amurka da dalar Amurka tiriliyan 2.4 cikin sama da shekaru 10, yayin da adadin kudin ruwa da kasar za ta biya zai kai dalar Amurka biliyan 551. Kazalika, kaso 89.3 bisa dari na masu bayyana raayoyin sun nuna damuwar cewa, kudurin dokar zai haifar da hauhawar hadarin bashi da Amurka ke fuskanta, tare da yiwuwar ingiza kasar cikin yanayi na komadar tattalin arziki. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp