Kasar Amurka na fitar da “Ka’idojin ingancin dimokaradiyya”, kana tana ingiza “sauyin dimokaradiyya ” a sassan duniya, wanda hakan ke haifar da rashin daidaito, da tashe tashen hankula da bala’u.
Sakamakon wasu kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN, da hadin gwiwar jami’ar Renmin ta Sin, karkashin cibiyar nazarin harkokin sadarwar kasa da kasa ta “New Era”, ya nuna yadda masu bayyana ra’ayoyi daga kasashe daban daban suka bayyana matukar rashin gamsuwa, da yadda Amurka ke amfani da batutuwan dimokaradiyya wajen danne kasashe da nufin cimma burikan kashin kai, da ma yadda matakin Amurkan ke kara fadada rarrabuwar kawuna tsakanin sassa daban daban na duniya, da kuma haifar da fadace-fadace tsakanin bangarori mabanbanta.
- Yadda Dimokaradiyya Ke Aiki A Kasar Sin
- Sin: Bai Kamata ‘Yancin Fadin Albarkacin Baki Ya Zama Kafar Nuna Kiyyaya Ga Musulmai Ba
Kaza lika, kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ta nuna cewa, kaso 71 bisa dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyin su sun soki Amurka, bisa yadda take tsoma hannun ta cikin harkokin gidan sauran kasashe, da danne sauran kasashe ta hanyar fakewa da “dimokaradiyya”.
Kaso 68 bisa dari na masu bayyana matsayar sun damu, da yadda Amurka ta shafe tsawon lokaci a tarihi ta na rura wutar “juyin juya hali”, da hura wutar “yakin bayan fage” a sassan duniya masu yawa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp