Fitaccen malamin nan na Hausa kuma mai nazarin wakoki a Jami’ar Jihar Kaduna, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook kan kalaman mawaki Rarara kan shugaba Buhari da gwamnatinsa.
Malumfashi ya ce, kuskuren da yawanci ke yi game da batun Rarara bai wuce ana yi masa kallon Maroki ko Mawaki ba ne kurum!
- ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Tara Min Kudi Don Yi Wa Tinubu Waka Saboda Kaunarsa -Mawaki Rarara
- Rarara Ya Bukaci Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Ake Masa
Wasu kuma na ganin ai bai ma da ilimi ko mutanen da zai iya bugun gaba da su, a ce ya zama wani abu a jam’iyyar APC ko siyasar Nijeriya.
Kuskure ne a ɗauki irin wannan mutum da baiwar da Allah ya yi masa da tasirin da baiwar take da shi a farfajiyar zamantakewa da siyasar Arewacin Nijeriya, a matsayin ɗan ƙauyen Kahutu da ya sami dama, wanda cikin kusan shekara 15 ya zama ɗan ma’abban da ke naɗa Sarki da muƙarrabansa.
Kuskure ne a yi tunanin cewa ba zai iya juya lamurra da baiwarsa a yanzu ba, kamar yadda ya yi a baya. Iska fa ta kaɗa a cikin watannin da wannan gwamnati ta yi, kuma tuni iskar ta bayyana zumɓutun kaza kowa na gani.
Kuskure ne a ce jam’iyyar APC da jiga-jiganta ba su san irin lalatar da ke ƙunshe a cikin kalangai da zaƙin muryar RARARA ba.
Idan har ba a fahimci zancen ba, a tambayi Jonathan ko Shekarau ko Kwankwaso ko Shema da irin su da dama, a tsawon lokaci. Idan sun ƙi tankawa, ai magoya bayansu ba za su manta ba!
Kuskure ne a ɗauka RARARA ba kowan komi ba ne!