Jiya ne, kwalejin Confucius dake jami’ar kasar Saliyo, ya yi bikin cika shekaru 10 da fara aiki a kasar.
Darektar kwalejin Confucius na jami’ar Saliyo Jing Man, ta bayyana cewa, tun daga shekarar 2012 zuwa yanzu, kwalejin ya kafa sassan koyarwa guda 20, yayin da adadin daliban da suka yi rajista ya karu cikin sauri.
Ta kara da cewa, tasirin kwalejin Confucius da ke kasar Saliyo ya karu, kuma a yanzu haka, kwalejin na taka muhimmiyar rawa wajen inganta harshen Sinanci da al’adun kasar Sin a kasar.
Jing ta ce, kwalejin zai ci gaba da baiwa dalibai guraben yin karatu a kasar Sin, da samar da karin guraben ayyukan yi ga ‘yan kasar Saliyo don su yi aiki a kwalejin.
A nasa jawabin, mataimakin ministan fasaha da ilimi mai zurfi na kasar Saliyo Sarjoh Aziz Kamara, ya ce kwalejin zai kasance wata babbar kafa ta fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu.
Mohamed Sheriff dake zama wakilin jami’ar Saliyo, ya bayyana cewa, jami’ar za ta baiwa kwalejin cikakken goyon baya, domin samun kyawawan nasarori. (Ibrahim)