Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Uwargida Sarautar Mata.
A yau shafin namu zai tabo mana kwalliyar uwargida a cikin gidanta:
Kwalliya wata aba ce da take kara wa mace kyau duk kyan mace idan ta yi kwalliya za ta kara kyau idan wadda tasaba da kwalliyar ce daidai da rana daya idan ba ta yi ba sai an ganta wata iri, haka zalika duk munin mace idan ta yi kwalliya za ta yi kyau saboda haka kwalliya tana daya daga cikin babban abu na gyaran mace.
Uwargida mu daure muna kwalliya a cikin gidammu na aure sai ki ga idan mace ta yi aure wai shike nan ta bar kwalliya kullum idan ka shiga gidanta kamar an tono ta a rami wai ita matar aure. Za ki ga da kafin ta yi aure ita uwar kwalliya ce har ma da kayan kwalliya take yawo a cikin jaka a jima a goga, amma ta yi aure ta bari maimakon a ce ai yanzu ne ma za’a fara kwalliya tun da kin yi aure kina da wanda za ki yi wa ya gan ki ya ji dadi ki samu lada ki yi wadda tafi tada lokacin yana zuwa zance.
Kwalliya ido ce ga mace kwalliya tana gyara mace tana kara wa mace daraja da kima a idon maigida.
Amma sai ki ga matar aure in an ganta da kwalliya to fita za ta yi shi ne za ta yi kwalliya har sai ki ji yara daga sun ganta da kwalliya suna cewa mama za ki biki ne? wato fita za ta yi shi ne ta yi kwalliya.
Akwai wani kuskure da muke yi wai ba ya yaba kwalliya ta shi ya sa ba zan yi ba, tabbas akwai zafi ki dage ki takarkare ki bata kusan awa daya kina yi wa maigida kwalliya amma sai ki ga wani idan ya shigo ko kallon inda kike ba zai yi ba, ballantana ya ce kin yi kyau wannan kalmar tana yi wa maza nauyi a baki, sannan kuma gaskiya da ciyo. To amma me kar ki damu da sai ya yaba ki ke kanki kin ji dadin kin yi kyau, sannan kuma ko gaban madubi kika je kin san kin yi kyau, to wannan ya kara miki karfin gwiwar yi, shima kansa ya ji dadi ya san kin yi kyau kawai ya budi baki ne ya ce kin yi kyau yake masa nauyi idan kin ga kin yi kyau wannan ya kara miki karfin gwiwar gobe ma ki sake wadda tafi wannan.