Tawagar Kungiyar Kwallon Kafa ta Mata ta Nijeriya, Super Falcons ta yi rashin nasara a hannun mai masaukin baki, Morocco a wasan da aka kammala yanzu-yanzu.
Nijeriya ta yi rashin nasara ne a bugun da kai sai mai tsaron raga, inda ta barar da kwallo daya, yayin da Morocco ta ci nata duka guda 4.
Tun da farko sai da aka fafata na tsawon minti 90 babu ci, sannan aka kara lokaci tsawon minti 30, nan ma aka yi kare jini biri jini babu ci.
Nijeriya ta samu nakasu a wasan inda aka kori ‘yan wasanta biyu da jan kati saboda ƙeta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp